Alhazan Najeriya sun koka kan rashin kwasarsu zuwa gida

Yanzu haka wasu Alhazan Nijeriya suna can sun shiga wani mawuyacin hali a birnin Madina na kasar Saudiyya, bayan da hukumar Alhazan Nijeriar ta kasa kwashe su zuwa gida a yau, kamar yadda ta yi musu alkawari.

Alhazan sun ce sun yi wata tattaunawa da wakilan Hukumar Alhazan ta Nijeria a jiya, amma ba su sake ganinsu ba.

Kusan ko wacce shekara dai a kan samu matsaloli wajen jigilar Alhazan Nijeriya zuwa gida inda da dama daga cikinsu ke shiga halin kaka na ka yi a kasar ta Saudiyya.

Makonni uku kenan dai da kammala aikin Hajjin bana.

Sai dai hukumar alhazan ta jaddada cewar tana kan shirin kwashe mahajjatan a kan lokaci nan da 18 ga watan nan.