Kungiyar Ecowas ta umurci Shugaba Gbagbo da ya san inda dare yayi masa

Tambarin kungiyar Ecowas
Image caption Tambarin kungiyar Ecowas

Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afrika ta ECOWAS/CEDEAO ta dakatar da kasar Ivory Coast daga cikin kungiyar saboda kin da shugaban kasar mai ci Laurent Gbagbo ya yi na amincewa da cewar ya sha kaye a zaben watan da ya wuce.

A wajen wani taron koli na musamman a Najeriya, kungiyar ta ECOWAS ta amince da cewar Allasanne Outtara ne sabon zababben Shugaban Ivory Coast, sannan ta bukaci Mr Gbagbo da ya sauka daga kan karagar mulki ba tare da wani bata lokaci ba.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ne ya bayyana haka a karshen wani taron koli na musamman a kan rikicin zaben kasar ta Ivory Coast da kungiyar ta yi a Abuja.

Yanzu haka dai Laurent Gbagbo bai da alamar sauka, inda tuni ya rantsar da majalisar zartarwarsa.