An kasa cimma yarjejeniya a Gabas ta tsakiya

Baya ga duk yunkurin da gwamnatin shugaba Obama na Amurka ke ci gaba da yi domin ganin an sake komawa teburin tattaunawa a tsakanin Israela da Palasdinu, lamari dai ya kusa kaiwa ga makura.

Duk da irin yunkurin da gwamnatin Obama ta shafe tsawon lokaci tana yi tun bayan hawan ta kan mulki har yanzu babu wani abin a zo a gani da ya biyo baya.

Wadansu masu sharhi akan al'amura dai na ganin cewa hanyar da gwamnatin Obama ke bullowa al'amuran sun dogara ne akan wadansu kura kurai.

Wadansu sun kalubalanci dakatar da gina matsugunnan yahudawa 'yan kama wuri zauna da ya kasance sharadi a yarjejeniyar zaman lafiyar da ake son cimmawa.

Wasu kuma sun ce dakatar da gine ginen wani abu ne da ya zama lallai, tun da dai batun ya raja'a ne akan gine ginen matsugunnan yahudawa 'yan kama wuri zauna da Israela ke yi.

Abin dai da yake a bayyane shine wasu na ganin da a ce gwamnatin Obama, kamar yanda ta kai ziyara birnin Alkahira da Istanbul, to da ta kai wata Israela domin yin magana gaba da gaba da su.

A yanzu dai kam ya zama lallai Amurka ta aminta da rashin nasarar da ta samu wajen cimma yunkurin da ta ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin, lamarin da ya taso da ayar tambaya akan irin matsalolin da Amurka ke fuskanta ta fuskar diplomasiyyarta.