Australia ta dora alhakin bayanan Wikileaks kan Amurka

Kevin Rudd ad Clinton
Image caption Australiya ta dora alhakin Wikileaks kan Amurka

Ministan harkokin wajen Australia, Kevin Rudd, ya kare Julian Assange, dan kasar Australiar da ya kirkiro shafin intanet na Wikileaks, ya na mai cewar, Amirka ce ya kamata a dora wa laifi, dangane da dubban bayyanan sirrinta na diplomasiyya, wadanda aka wallafa ba bisa ka'ida ba.

Mista Rudd ya ce, mutanen da tun farko suka tsegunta bayyanan sune ya kamata a tuhuma, ba wai Julian Assange ba, wanda ya wallafa su ba.

Da alamun kalaman na Ministan harkokin wajen Australiar sun sabawa wadanda Praministar kasar, Julia Gillard tayi, inda ta zargi Julian Assange da matukar nuna rashin sanin ya kamata.

Ana ci gaba da tsare Julian Assange a London, yayinda hukumomin kasar Sweden ke neman a mika masu shi domin ya fuskanci shari'a, dangane da zargin yin fyade.

Masu satar bayyanai ta na'ura mai kwakwalwa sun kaddamar da hare-hare a kan kungiyoyin da suka daina karbar irin gudunmawar da Wikileaks ke samu.