Binciken BBC dangane da cin hanci da rashawa

Matsalar cin hanci da rashawa a duniya
Image caption Matasalar cin hanci da rashawa shine wani batu da jama'a suka fi tattaunawa akai a kasashen duniya

Wani binciken jin ra'ayoyin jama'a na kasa da kasa da BBC ta bada umurnin a gudanar, ya nuna cewa cin hanci da rashawa da ake tabkawa tsakanin jami'an gwamnati shine batun da aka fi tattaunawa akai akai a kashashen duniya.

Binciken wanda aka wallafa a dai dai lokacin da ake bukin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware, ya gano cewa, matsalar cin hanci da rashawa, da kuma handama tsakanin jami'an gwamnati shine batun da akasarin iyalai da abokai ke tattaunawa akai akai, fiye da matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da, talauci da rashin aikin yi, kai harma da batun hauhawar farashin kayayyakin abinci dana makamashi.

Wakilin BBC yace binciken, ya tattara ra'ayoyin mutane dubu talatin a kasashe ashirin da shida

Kowanne mutum daya cikin mutane biyar da aka ji ra'ayoyinsu, na cewa suna tattauna batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da abokai ko kuma iyalai a cikin watan daya gabata.