Fursunoni 81 sun halaka a kasar chile

Gidan yarin kasar Chile da kone
Image caption Bursunoni 81 sun halaka a gobarar gidan yari a kasar Chile

A kalla fursunoni 81 sun hallaka a Santiago, babban birnin kasar Chile, sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan kurkuku mai cunkoso.

An kwashe wasu 'yan kason kimanin 200 daga gidan yarin na San Miguel, wasunsu da munanan raunuka, saboda konewar da suka yi.

Da sanyin safiyar yau ne gobarar ta tashi, amma a halin yanzu an samu an kashe ta.

Ana tsammanin cewa gobarar ta tashi ne, a lokacin fadan da ya barke tsakanin kungiyoyi masu gaba da juna na fursunonin, wadanda suka cinnawa katifu wuta.

Daruruwan jama'a sun yi dafifi a gaban gidan kurkukun, domin ganin ko an rutsa da 'yan uwansu.