EFCC ta shigar da kara kan Dick Cheney

Dick Cheney
Image caption Ana zargin yunkurin bada cin hanci ga wasu jami'an Najeriya Dick Cheney

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta shigar da kara a kotu tana tuhumar tsohon mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney, bisa yunkurin bada cin hanci ga wasu jami'an Najeriya.

Mista Cheney na daya daga cikin mutane taran da ake zargi da aikata laifin, fiye da shekaru goma da suka wuce, a lokacin da yake babban darektan kamfanin mai na Halliburton.

Dick Cheney ya musanta dukan zargin. Lauyansa ya ce, jami'an Amurka sun gudanar da bincike sosai a kan lamarin, kuma basu gano wata alamar da ta nuna cewa ya aikata wani laifi ba.

Ana zargin Halliburton da bayar da cin hancin dala miliyan 180 ga jami'an Najeriya, domin samun kwangilar dala biliyan 6, ta gina wata cibiyar sarrafa iskar gas a kasar.