Kwamitin tsaron MDD ya goyi bayan Alassane Ouattara

Kasar Ivory Coast
Image caption Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kammala tattaunawa tare da nuna goyan bayansa ga Alassane Ouattara a matsayin zabebben shugabankasar Ivory Coast

Bayan shafe kwanaki yana tattaunawa, kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya nuna goyon bayansa ga dan takarar jam'iyar adawa a kasar Ivory Coast Alassane Outtara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ake takaddama a kai.

Matsayin da kwamitin tsaro na Majalisar ya dauka duk da adawar da kasar Rasha ta nuna akai dai, ya kara karfafa allawadai da ake tayi daga kasashen duniya kan matakin da shugaba Laurent Gbagbo ya dauka na yin biris da kiraye kirayen da ake masa na ya sauka daga karagar mulkin kasar.

Wakiliyar BBC ta ce wasu jami'an diflomasiyya sun bayyana cewa kasar Rasha ta dage cewa nuna goyan baya ga wani mutum daya a zaben da ake takaddama akai ya wuce ikon da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniyan keda shi.