Kasashe 6 na ganawa akan cutar Noma

Niger

A Jamhuriyar Niger an bude wani taron kwarrarun likitoci masu aikin yaki da zutar Cizal ko kuma Noma a Faransance.

Kasashe 6 ne na Africa ta Yamma wadanda suka hada da Senegal, Mali, Burkina da Jamhuriyar Niger suka shirya taron.

Taron wanda zai dauki kwanaki ukku ana yi, zai yi kokarin lalubo hanyoyin tsara wasu shirye shirye na hadin gwiwa tsakanin kasashen domin maganin cutar ta Cizal ko Noma.

Akwai daruruwan yara a Jamhuriyar Niger da ke amfana daga aikin tiyatar da wata kungiyar kasar Jamus mai suna Hilfisktion Noma ta ke yi a kyauta.