An kammala rajistar masu kada kuri'a a kudancin Sudan

Kasar Sudan
Image caption Kimanin mutane miliyan uku ne aka yiwa rijistar kada kuri'a a kudancin kasar Sudan

An kammala rajistar masu kada kuri'a a kudancin kasar Sudan gabannin zaben raba gardamar da aka shirya gudanarwa a watan Janairu.

Zaben raba gardamar dai zai yanke hukunci a kan ko yankin na bukatar samun 'yancin kai.

Rahotanni sun ce kimanin mutane miliyan uku ne aka yiwa rajistar kada kuri'a a kudancin kasar, koda yake mutane 'yan kalilan ne dake arewacin Sudan din suka yi rajistar, ba kamar yadda ake zato ba.

Wakilin BBC ya ce ana ci gaba da zaman dar dar a dai dai lokacin da zaben raba gardamar ke kara karatowa.

Tsofaffin 'yan tawaye a kudancin Sudan dau sun zargi arewacin kasar da jefa bama bamai a wasu yankunan kudancin kasar a lokuta da dama.