Masu goyan bayan Wikileaks sun gurgunta shafin Master Card

Master Card

Masu goyan bayan shafin nan na Wikeleaks da ke kwarmata bayanan sirri sun ce sun yi illa ga wasu shafuka na kamfanonin hada hadar kudi, saboda hadin kan da suka ba Amurka domin yi masa zagon kasa.

Masu satar shiga shafukan Internet sun hana shafin kamfanin katin bashi na Master Card yin aiki, a wani mataki na ramuwar gayya.

Shi dai kamfanin Master Card ya dakatar da hulda da shafin Wikileaks.

Har ila yau kungiyar masu goyan bayan shafin na Wikileaks, mai suna Operation Payback ta ce ta haddasa cikas ga shafukan kamfanin katin bashi na Visa, da bankin Swiss Post finance da kuma Paypal.

Wani babban jami'in kamfanin PayPal, ya ce kamfanin ya dakatar da yin hulda da shafin Wikileaks ne a sakamakon wata wasika da gwamnatin Amurka ta tura musu.