Cin hanci da rashawa na kara samun gindin zama a duniya

Image caption Mutane da dama na ba 'yan sanda cin hanci

Wani bincike ya yi nuni da cewa rashawa na kara samun gindin zama a duniya a shekaru uku da su ka wuce.

Kashi hamsin da shida cikin dari na mutanen da kungiyar Transparency International ta yi hira da su sun ce ana kara samun rashawa a kasashen duniya.

Kungiyar ta sanya kasashen Najeriya da Iraki da kuma Indiya a matsayin kasashen da rashawa ta fi katutu a yayinda kasar China da Rasha da kuma akasarin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ke biye da su.

Wani binciken jin ra'ayoyin jama'a na kasa da kasa da BBC ta bayar da umurnin a gudanar ya nuna cewa cin hanci da rashawan da ake tafkawa a tsakanin jami'an gwamnati shi ne batun da aka fi tattaunawa a kai a kashashen duniya.

Binciken da BBC ta gudanar

Binciken, wanda aka wallafa a daidai lokacin da ake bukin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, ya gano cewa matsalar cin hanci da rashawa, da kuma handama a tsakanin jami'an gwamnati shi ne batun da akasarin iyalai da abokai ke tattaunawa a-kai-a-kai.

An dai fi tattauna batun fiye da matsalolin da suka shafi sauyin yanayi, da talauci, da rashin aikin yi, kai har ma da batun hauhawar farashin kayayyakin abinci da na makamashi.

Kowanne mutum daya a cikin mutane biyar da aka ji ra'ayoyinsu ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da abokai ko kuma iyalai a cikin watan daya gabata.

Batun cin hanci a duniya

A binciken da Transparency International ta gudanar, ta gano cewa rashawa ta fi muni a jam'iyyun siyasa, kuma kashi hamsin cikin dari na mutanen da aka yi hira da su sun ce gwamnatoci sun kasa magance matsalar.

Kowanne daya daga cikin rukunin mutane hudu da aka yi hira da su ya yi nuni da cewa ya bayar da cin hanci, kuma 'yan sanda ne su ka fi karbar cin hanci.

Kashi ashirin da tara cikin dari na cin hancin da aka bayar dai ya shiga hannun 'yan sanda ne a yayinda kashi ashirin cikin dari ya shiga hannun jami'an yin rajista da kuma bayar da izini; sai kuma kashi goma sha hudu cikin dari da ya tafi bangaren shari'a.

Me ya sa ake ba da cin hanci?

Mutane daga kasar Afghanistan da Najeriya da Iraki da kuma Indiya sun fi fuskantar rashawa a rayuwarsu ta yau da kullum.

Rabin mutanen da aka yi hira da su a kasashen sun bayana cewa sun bayar da cin hanci a shekarar da ta wuce.

Ana dai ganin kashi tamanin da hudu cikin dari na mutanen Cambodia da kashi tamanin da tara cikin dari a Liberia su ma sun bayar da cin hanci.

A kasar Denmark ba a samu rahoton cin hanci ko guda ba.

Daraktar bincike da kuma tsare-tsare na kungiyar Transparency, Robin Hodess, ta ce kungiyar ta damu matuka game da batun cin hanci a duniya.

"Abin damuwa shi ne yadda mutane su ka fi ba 'yan sanda cin hanci.

"Yawan mutanen da ke bayar da cin hanci ya karu ninki biyu a cikin shekaru biyu".

Kimanin kashi hamsin da shida na mutane a yankin kudu da sahara ne ake ganin sun bayar da cin hanci.

Masana sun alakanta cin hanci da rashawa a duniya ga tabarbarewar yanayin tattalin arzikin duniya.