An yi musayar wuta a Maiduguri

Ofishin 'Yan Sanda

Rahotanni daga jihar Borno a arewacin Najeriya sun ce an yi wata musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da yan Kungiyar nan ta Boko Haram a unguwar Zannari dake cikin garin Maiduguri.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne kan jami'an sojoji da yan-sandan dake da sansani a wannan unguwa da misalin karfe bakwai na safe.

Al'amarin ya dimauta mazauna unguwar sakamakon karar bindigogi da aka yi ta ji ba kakkautawa.

Baya ga musayar wutar yan bindigar, sun kone daya daga cikin motocin jami'an tsaron kurmus a yayinda rundunar 'yan sandan ta ce jikkata daya daga cikin 'yan bindigar.boko