Kungiyar AU ta dage takunkumin data sanyawa Guinea

Shugabankasar Guinea Alpha Conde
Image caption Kungiyar hada kan kasashen Afirka AU ta dage takunkumin data sanyawa kasar Guinea shekaru biyu da suka gabata

Kungiyar tarayyar Afrika ta dage takunkumin data sanyawa kasar Guinea shekaru biyu da suka gabata biyo bayan juyin mulkin soji da aka yi a kasar.

Hakan dai ya biyo bayan tabbatar da jagoran 'yan adawa Alpha Conde, da aka yi ne a makon daya gabata a matsayin zababben shugaban kasar.

Wakilin BBC ya ce zababben shugaban kasar ya ce ya shirya kafa hukumar tantance gaskiya tare da sasanta tsakani don magance matsalolin da suka haddasa tashe tashen hankula bayan zaben shugaban kasar tare kuma da keta hakkokin bil'adama da aka tabka a shekarun baya.