An sace na'urorin yin rajistar masu zabe a Nigeria

Shugaban Hukumar Zabe

Hukumar zabe ta Nijeriya ta ce wasu 'yan fashi da makami sun sace na'urorin yin rajistar masu zabe, jim kadan bayan kawo su Nijeriya a filin saukar jiragen sama na Lagos.

Wani mai magana da yawun hukumar zaben, ya ce an yi awon gaba da na'urorin kwamputa, da na daukar hoto, da sauran wasu abubuwa.

Sai dai jami'in ya ce satar ba zata yi matukar illa ga aikin rajistar masu kada kuri'a miliyan saba'in da aka shirya gudanarwa a Nijeriyar cikin watan gobe ba, gabanin babban zaben da aka shirya yi a shekara mai zuwa.