Jonathan ba shi da kwarewar shugabancin Najeriya - Wikileaks

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Bayanai na baya-bayan nan da shafin intanet na Wikileaks mai kwarmata bayanan sirrin da aka tsegunta masa ya wallafa, sun bayyana irin rawar da Amurka ta taka a lokacin da Mr Goodluck Jonathan yake matsayin mukaddashin shugaban Nigeria a yayinda shugaba na wancen lokaci Umar Yar'adua yake jinya.

Bayanan sun ambato Goodluck Jonathan da cewar ya na kokarin shawo kan jama'ar Arewacin Najeriya wadanda ba su saki jiki da shi ba, ta hanyar amfani da wasu manyan mutanen yankin arewan, musamman tsohon shugaban Nigeria Abdussalami Abubakar wanda zai lallashi iyalin 'Yar Adua, su saka shi, ya yi murabus cikin daraja da mutunci. Haka kuma zai bi shawarar Amurka ta nisanta kansa da Olusegun Obansanjo.

Jakadiyar Amruka a Najeriya a lokacin Robin Saunders ta gana da mukaddashin shugaban kasar Najeriya a lokacin wato shugaban yanzu Goodluck Jonatahan ranar 26 ga watan Fabrairun bana, jim kadan bayan da marigayi shugaba 'Yar'adua ya koma Najeriya daga Saudiyya inda yayi jinya.

Jonathan ya kuma fada mata cewa a saninsa jam'iyyar PDP ta zabe shi ne a matsayin abokin takarar shugaba 'YarAdua a 2007 saboda yana wakiltar yankin Niger Delta.

Ya ce "ba an dauke ni ba ne na zama mataimakin shugaban kasa saboda ina da wata kwarewa ta siyasa. Ba ni da ita. Da akwai mutane da dama da suka fi cancanta su zama mataimakin shugaban kasa, sai dai kuma wannan ba yana nufin wani zai iya juya ni ba.

Bayanan suka ce Goodluck Jonathan ya ce yana kokarin shawo kan jama'ar Arewacin Nigeria wadanda ba su saki jiki da shi ba, ta hanyar amfani da wasu manyan mutanen yankin arewan, musamman tsohon shugaban Nigeria Abdussalami Abubakar wanda zai lallashi iyalin 'Yar Adua, su saka shi, ya yi murabus cikin daraja da mutunci.

Hakan in ji Goodluck zai fi sauki a madanin samun goyon bayan kashi 2 cikin 3 na majalisar ministoci mai mutum 42. Ya kuma bayyana yadda a wani zaman majalisar minitocin aka tashi baram-baram inda aka yi ife-ife.

Goodluck ya dora laifin rudani a kan mutane hudu

Goodluck ya dora laifin rudanin da aka shiga a Najeriya a lokacin kan mutane hudu dake kewaye da 'Yar Adua, wato uwargidansa Turai 'Yar Adua, da babban mai tsaron lafiyar sa Yusuf Tilde da dogarin shugaba 'YarAdua Mustapha Onoe-dieva da Tanimu Kurfi mai baiwa marigayin shawara kan harkokin tattalin arziki.

Image caption Marigayi Shugaba, Umaru Musa Yar'adua

Haka kuma ya ambaci Abba Ruma ministan ayyukan noma da Adamu Aliero ministan birnin Abuja a matsayin wasu masu hana ruwa gudu.

Goodluck Jonathan yace ya yarda wadannan mutane suna da wata muguwar aniya, tun da yayi imanin cewa shugaba 'Yar Adua baya cikin hayyacinsa.

A game da yadda zai tunkari warware dambarwar siyasar Najeriya kuwa mukaddashin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce zai mai da hankali kan shirya zabe na fisa-bi-lillahi.

Kuma baya tsinkayen zai tsaya takarar shugaban kasa a 2011, kodayake dai a cewarsa "idan suna so in tsaya, to wannan wani abu ne da zan nazarta".

Kuma jakadiyar Amruka ta bayyana masa cewa wajibi ne ya sallami shugaban hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC, Prof Maurice Iwu saboda baya nuna wata alama ta mutunta tsarin mulki na gari.

Jakadiyar ta yi barazanar cewa muddin Goodluck bai kori Iwu ba, to gwamnatin Amurka zata janye duk wani tallafi na shirin zabuka a Nigeria.

Bayanan na Wikileaks sun ce jakadiyar Amurka ta kuma baiwa Mukaddashin shugaba Goodluck shawarar nisanta kansa da tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, kuma Goodluck ya ce zai yi hakan.

Najeriya ta karyata Wikileaks

Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata bayanan na Wikileaks inda ta ce shafin bai bayyana sahihin abun da ya faru tsakanin shugaba Goodluck Jonathan da kuma jakadar Amurka Robin Sanders ba.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa Shawara kan harkarkokin yadda labarai, Mista Ima Niboro, gwamnatin Najeriyar ta ce babu yadda za a ce shugaba Jonathan ya shaidawa jakadar Amurka cewa ba shi da kwarewar da zai jagoranci Najeriya.

Sanarwar ta ce; " Ya za a ce shugaba Jonathan ba shi da kwarewa, bayan ya taba rike mukamin mataimakin gwamna, ya rike mukamin gwamna, kafin ya zama mataimakin shugaban kasa, sannan ya zama mukaddashin shugaban kasa."

"Shugaba Jonathan na rike da shaidar digiri na uku, kuma ya yi aikin malamin jami'a na tsawon shekaru goma, duk wanda ya rike wadannan mukaman babu yadda za'a ce ba shi da kwarewa."

Sanarwar ta kara da cewa an wallafa bayanan ne da san rai, kuma gwamnatin Najeriya ba ta ji dadin yada hakan ya auku ba, inda ta ce za ta bi hanyoyin da suka dace domin warware matsalar ta fannin diplomasiyya.

Kamfanin Shell na leken asiri a Najeriya

Image caption Kamfanin Shell

Bayanan da shafin na Wikileaks ya kwarmata sun kuma ambato babbar jami'ar kamfanin Shell a Najeriya a lokacin Ann Pickard tana shaida wa jami'an Diplomasiyyar Amurka a Abuja cewa kamfanin Shell ya samo bayanan sirrin gwamnatin Najeriya da ke nuna cewa gwamnatin na gayyatar kasar China ta zo ta zuba jari a harkokin man Najeriya.

Bayanan da aka kwarmata sun ambato Jami'ar ta Shell tana shaida wa Jakadiyar Amurka a Najeriya ta lokacin Robin Sanders cewa, gwamnatin Najeriya ta manta cewa kamfanin Shell ya daddasa ma'aikatansa a dukkan muhimman ma'akatun gwamnati kuma ta dalilin hakan Shell yana da cikakkun bayanai a kan dukkan abubuwan da ake yi a ma'aikatun.

Bayanan da jaridar Guardian ta Ingila ta wallafa sun nuna cewa jami'ar ta Shell ta yi kokarin musayar bayanai na sirri da jami'an Amurka kan aikace-aikacen masu tada kayar baya a yankin Naija Delta, wadanda suka yi tsanani a shekarar 2006, kafin shirin yin afuwar gwamnati ga 'yan bindigar ya kawo saukin al'amuran a bara. Jami'ar ta Shell Ann Pickard ta bayyana cewa kamfanin yana da bayanan sirri da ke nuna cewa an shigar wa da masu tada kayar bayan makamai masu linzami daya zuwa uku, sai dai ba ta da cikakken tabbaci a kan hakan.

Wani abun arashi shi ne kamfanin na Shell a lokacin ya nuna dari-darin musayar bayanai da jami'an gwamnatin Amurka saboda in ji Shell, gwamnatin Amurka tamkar rariya take wajen adana bayanan sirri.

Kamfanin NNPC ya mayar da martani

A martanin gwamnatin Najeriya dangane da batun, an ambato mai magana da yawun kamfanin mai na kasar NNPC Levi Ajunoma yana cewa, kamfanin Shell ba ya iko da gwamnatin Najeriya, wadannan bayanan da aka kwarmata karya ne kuma kokarin kaskantar da gwamnatin Najeriya ne.

Shi ma mai magana da yawun kamfanin Shell Precious Okolobo, ya ce bayanan da aka wallafa cewa kamfanin na leken asirin gwamnatin Najeriya ba gaskiya bane.

A nasa bangaren, ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya ce ba zai kara komai a kan martanin da sakatariyar harkokin wajen Amurkan Hillary Clinton ta mayar tun da farko a kan batun bayanan da aka kwarmata ba.

Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Ita dai Hillary Clinton ta ce wallafa bayanan da Wikileaks ya yi tamkar wani hari ne ya kaddamar a kan al'ummomin duniya. Kuma tuni Amurkan ta umarci jami'anta da su kara tsaurara tsaro kan bayanan sirri.

Masana a kan harkokin man Najeriya dai ba za su yi mamakin bayanan da aka wallafa ba, ganin cewa ma'aikatan Shell da dama na aiki a wurare masu muhimmanci a Najeriyar, kuma sanannen abu ne cewa akwai aikace-aikace na hadinn gwuiwa da akan yi tsakanin kamfanin mai na kasa NNPC da kuma kamfanonin kasashen waje da ke aikin mai a kasar ciki har da shell.

Wadannan aikace aikacen kan kunshi musayar bayanan sirri daga bangarorin biyu.

Najeriya dai ita ce ta gaba-gaba wajen samar da man fetur a nahiyar Afrika, kuma kamfanonin kasashen waje irinsu Shell, Mobil da Total su ne suka yi kaka gida a harkokin man kasar tsawon shekaru da dama.