Jama'a na yin gudun hijira daga Cote d'Ivoire

Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara
Image caption Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane kimanin 2000 sun tsere daga Cote d'Ivoire, bayan zaben shugaban kasar na watan jiya, wanda ya janyo takaddama.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar ta ce, galibinsu sun warwatsu a wasu kauyuka dake makwabtaka da kasashen Liberia da Guinea.

'Yan gudun hijirar sun shaidawa majalisar cewa, sun tsere ne saboda fargabar da suke da ita, cewar tashin hankali na iya barkewa idan takaddamar siyasar ta ci gaba. A jiya ne Tarayyar Afirka ta dakatar da Cote d'Ivoire - bayan kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ita ma ta dauki irin matakin - tana mai cewa dan adawa Alassane Ouattara ne ya lashe zaben.

A yanzu haka dai kasar ta Cote d'Ivoire tana da shugabanni biyu ne - watau Laurent Gbagbo, wanda rundunar sojan kasar ke marawa baya, da kuma Alassane Ouattara, wanda majalisar dinkin duniya ta ce shine ya yi nasara a zaben da aka gudanar a kwanan nan.