An kaddamar da shirin riga kafin sankarau a Nijar

Kwayar da ke haddsa sankarau

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da shirin yiwa al'umma riga kafin cutar sankarau.

Firayim ministan kasar ne Dr Mahamadu Danda ya jagoranci bikin kaddamarwar a unguwar Saga,daya daga cikin unguwannin kewaye birnin Niamey inda galibin masu karamin karfi ke zama.

Mutane kimanin miliyan 3 ne hukumomin ke sa ran za'a yiwa riga kafin.

A matakin farko, aikin zai shafi jihohin Niamey da Dosso gabanin shirin yakai ga sauran yankunan kasar.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ko OMS tare da wasu abokan arziki masu hannu da shuni ne ke taimakawa ga shirin wanda kuma zai shafi wasu kasashe da ke makwabtaka da Nijar kamar Mali da Burkina Faso.