Pfizer ya musanta zargin Wikileaks akan Najeriya

Tambarin Pfizer
Image caption Tambarin Pfizer

Kampanin harhada magungunan Amurka, Pfizer, ya musanta zargin cewa ya dauki hayar wasu masu bincike, domin su kwakwulo wasu bayanai na batanci a kan tsohon antoni janar na Najeriya, a kokarin matsa masa lamba domin ya dakatar da karar da aka kai kampanin, kan zargin gwajin magani ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa, kampanin Pfizer ya bayyana zargin, wanda ke kunshe cikin wasikun ofisoshin jakadancin Amurka, wadanda aka wallafa a shafin intanet na Wikileaks da cewa, abin takaici ne, maras kan gado.

A bara kampanin ya cinma yarjejeniya a wajen kotu da gwamnati, game da batun gwajin, wanda hukumomi ke zargin ya haddasa mutuwar yara kimanin 11.

Kampanin na Pfizer dai na musanta aikata ba daidai ba a gwajin na 1996.