An yi bukin bada kyautar yabo ta zaman lafiya ta Nobel

Thornjorn Jagland
Image caption Thornjorn Jagland

Shugaban kwamitin bada kyautar Nobel ta zaman lafiya ya ce akwai alaka tsakanin zamaa lafiya da kuma kare hakkin bil'adama.

Thorjorn Jagland ya bayyana haka ne a wajen bikin karrama mai fafutukar kafa dimokradiyyar nan dan kasar China dake daure, Liu Xiabao.

A jawabin da ya yi, shugaban kwamitin mika kyautar yayi kira ga hukumomin kasar ta China da su saki Mr Liu Xiaobo, daga daurin shekaru goma sha dayan da suke masa.

A wajen bukin an bar wata kujera da babu kowa a kanta domin girmama Mr Liu, wanda yanzu haka yake zaman sarka na shekaru sha daya a Chinar bayan an same shi da laifin kulla makarkashiya a kasar China.