Masar ta musanta satar masu kaura

Hosni Mubarak
Image caption Shugaban Masar

Kasar Masar ta musanta rahotannin da ke cewa masu safarar mutane a yankin Sina'i sun sace daruruwan masu kaura daga kasar Eritrea da ke kokarin shiga Isra'ila.

A makon jiya ne hukumar majalisar dinkin duniya da ke kula da masu kaura ta bayyana damuwa game da rahotannin da ke cewa an rufe wasu 'yan gudun hijira a nahiyar Afrika a cikin manyan akwatunan daukar kaya saboda gaza biyan kudin fansa.

Ministan hulda da kasashen waje na kasar Masar, Ahmad Abul Gheit ya musanta wannan batu.

Ya ce jami'an Masar din sun bincika rahoton amma ba su samu wata hujjar da ke nuni da faruwar lamarin ba.