An gano gawar Mark Madoff

gidan Madoff
Image caption 'Yan sanda a kofar gidan Madoff

An gano gawar daya daga cikin 'ya'yan dan damfarar nan na garin New York, Bernad Madoff, a lokacinda ake cika shekaru biyu da kama babansa.

'Yan sanda sun ce an gano gawar Mark Madoff ne a gidansa bayan da alamu ke nuna cewa shi ya rataye kansa.

Wakilin BBC Ian Mackenzie ya ce hukumomin kasar Amurka na binciken Mark Madoff da dan uwansa Andrew kan rawar da suka taka a damfarar.

Su biyun dai sun musanta cewa suna da hannu a ciki kuma kawo yanzu babu wata tuhuma da aka yi musu ta aikata laifi.

Sai dai masu zuba jarin da su ka yi asarar kudadensu sun shigar da kararrakin da suke bukatar yan uwan biyu su biyasu.