SPLM ta goyi bayan 'yancin kudancin Sudan

Dakarun SPLM
Image caption Dakarun SPLM

Jam'iyyar dake rike da gwamnatin kudancin Sudan wato SPLM, a karon farko ta fito ta bayyana goyon bayanta ga 'yancin yankin, ana saura wata guda a gudanar da zaben raba gardama kan batun.

Sanarwar ta sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2005 wadda ta kawo karshen shekara da shekaru da aka kwashe ana yakin basasa a kasar.

Wakilin BBC ya ce kakakin jam'iyyar Anne Itto ta tsaya ne a gaban pastocin dake nuna alamar 'yan kudanci su zabi yancinsu, wadda ita ce sanarwa mafi karfi da jam'iyyar SPLM ta taba yi.

Ta ce ba a girmama batun hadin kai ba, don haka SPLM za ta yi kamfe na ballewar yankin.