An hallaka sojojin Amurka 6

Sojojin NATO

An hallaka sojojin Amurka akalla shidda a wani hari da aka kai a kusa da birnin Kandahar a kudancin Afghanistan. Wannan hari ya kawo adadin sojojin kasashen wajen da aka hallaka a cikin wannan shekarar zuwa dari bakwai.

Wadannan sojoji suna kokarin taimakawa ne wajen duba wani wurin zirga-zirgar ababen hawa a birnin Kandahar, lokacin da bama-bama suka fashi.

Motar ta rusa katangar harabar da sojojin ke ciki, kamar yadda wadanda abun ya faru a kan idanunsu suka bayyana, inda kantangar ta fada kan sojojin na Amurka.

Al'amarin ya faru ne a kauyen Sangsar, wanda ke kusa da birnin Kandahar inda nan ne cibiyar kungiyar Taleban. Su dai sojojin na Amurka sun shafe watanni ukkun da suka wuce suna gumurzu tare da yan Taleban din a wannan yanki, a yunkurin da suke na fatattakar 'yan kungiyar ta Taleban.