Sojoji sun kaddamar da hari akan 'yan tawayen Darfur

Yankin Darfur
Image caption Sojojin gwamnati sun kaddamar da hare hare akan kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Sudan Liberation Army a yankin Darfur.

Sojojin samar da zaman lafiya na kasa da kasa dake Sudan sunce sojojin gwamnati sun kaddamar da hare hare na kwanaki biyu kan kungiyar 'yan tawayen Sudan Liberation Army a yankin Darfur.

An kashe akalla mutum daya, yayin da kuma mutane goma sha shida suka samu raunuka a hare haren da aka kai a kauyen Khor Abeche dake kudancin Darfur.

Rahotanni sunce an kuma kona gidaje da dama inda fiye da mutane dari biyu ne suka fice daga gidajensu.

Tun a farko wannan watan ne gwamnati kasar ta zargi 'yan tawayen da keta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla shekaru hudu da suka gabata, inda ta ce kungiyar ta aike da wasu mayakanta don su hadu da wasu kungiyoyin 'yan tawaye a Darfur.