Zaben majalisun dokoki a Kosovo

Zaben 'yan majalisun dokoki a Kosovo
Image caption Kasar Kosovo na gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a karon farko tun bayanda kasar ta ayyana 'yancin kai daga Serbia.

Wannan zabe dai shi zai kasance tamkar wani zakaran gwajin dafi na auna yadda dumukradiyyar Kosovo take.

Jam'iyyu ashirin da tara ne zasu fafata a zaben.

jamiiyyar PDK ta Fira Ministan kasar mai barin gado ita ce kan gaba a kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar .

Jam'iyyar LDK ce ke bi mata da kuma wasu jam'iyyu biyu da suke fatan suma su sami kuri'un wadanda basu gamsu da wadancan jam'iyyun biyu ba.

Rashin aikin yi a kasar ya kai kusan kashi arbain da biyar cikin dari , sai kuma rashin masu zuba jari 'yan kasashen waje, ga kuma matsalar cin hanci da rashawa data zama ruwan dare