Shugaban Senegal ya nemi da a sako Tandja

Abdoulaye Wade

A jamhuriyar Niger wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama sun fara tsokaci a game da kiran da Shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade, na neman a sako tsohon Shugaban Niger, Malam Tandja Mamadou.

Shugaban na Senegal, Abdoulaye Wade ya ce ci gaba da tsare sohon shugaban kasar na Niger ya sabawa tsarin dokokin kawancen tattallin arzikin Africa ta yamma watau Ecowas ko Cedao.

Wannan kira dai ya biyo bayan wani hukunci ne da kotun Ecowas ta yanke a farkon watan jiya inda ta umurci gwamnatin mulkin sojan Niger din da ta saki tsohon shugaban kasar na Niger.

Gwamnatin ta Niger ta ce tana ci gaba da nazari a kan wannan hukunci kuma mai yiwuwa ne ta daukaka kara.