Shafin intanet na BBC ya koma aiki a China

Shafin intanet na BBC ya koma aiki a China
Image caption China ta dade tana takaita damar samun bayanai

A yanzu mutane na iya samun shafin intanet na BBC a kasar China bayan da aka toshe shi na wani tsawon lokaci.

Toshe shafin ya zo daidai da bikin bayar da kyautar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ga wani mai fafutukar kare hakkin bil'adama dan kasar ta China, Liu Xiaobo.

An toshe shafin ne tare da wadansu shafuffukan kafofin yada labarai na duniya.

Gwamnatin China dai na toshe shafuffukan jefi-jefi, sannan ta kan takaita irin bayanan da mutane ka iya samu ta intanet a kasar.

Martani cikin fushi

Jami'ai a kasar ba su ce komai game da rufe shafin ba, kuma zai yi wuya su dauki alhakin lamarin.

Sai dai a fili take cewa China na aiwatar da irin wadannan ayyuka ne da nufin takaita bayanan da ke fitowa daga hanyar sadarwa ta intanet.

Wadansu shafuffuka, kamar na kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ba a iya samun su kwata-kwata a kasar ta China.

Sauran kuma, kamar na BBC, a kan rufe su jefi-jefi, idan akwai wani muhimmin labari wanda ke da alaka da China.

A wannan lamarin na baya-bayan nan, an toshe shafin intanet na sashen Ingilishi na BBC kwana guda kafin ranar da za a yi bikin bayar da kyautar ta Nobel. Haka kuma, an lalata hanyoyin samun labarai na gidan talabijin na BBC.

Mahukuntan China sun nuna damuwa sosai lokacin da aka bayyana Liu Xiaobo, wanda ke zaman gidan yari na shekaru 11 bisa laifin tunzura jama'a, a matsayin wanda ya lashe kyautar ta bana.

Kwamitin bayar da kyautar dai ya gudanar da biki domin girmama Mr Liu a birnin Oslo na kasar Norway.

China ta yi iya kokarin ta domin hana labaran bikin isa ga jama'ar kasar.