Berlusconi ya gargadi Majalisar Dokokin Italiya

Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi
Image caption Rikicin tattalin arziki na damun kasashen Turai da dama

Fira Ministan Italiya Silvio Berlusconi, ya yi gargadin cewa kasar za ta shiga cikin rikicin tattalin arziki idan masu adawa da shi suka yi nasara wajen kada kuri'ar kin amince wa da shi.

Ya yi maganar ne a jawabin farko da ya gabatar ga Majalisar Dokokin Kasar, kafin a kada kuri'ar raba gardama kan salon mulkinsa a ranar Talata.

Idan har aka amince da kudurin to babu makawa sai an gudanar da sabon zabe a kasar.

Berlusconi ya gaya wa Majalisar Dattawan kasar cewa Italiya na fuskantar matsalar tattalin arziki, don haka bai dace a taso da rikicin siyasa a wannan halin ba.

Kwarin giwa

Mista Berlusconi ya ce yana da kwarin gwiwar yin nasara a kuri'ar da za'a kada a gobe Talata.

Masu adawa da shi na zarginsa ne da rashin alkibla a shugabancinsa, kuma suka ce hakan da yawan abin kunyan da ke faruwa dangane da halayyarsa, sun sha shi zama matsala ga kasar.

Mista Berlusconi ya kuma ce karan tsana kawai aka dora masa.

Ya ce:''Ni ne mutumin da aka fi dorawa kahon-zuka a tarihin duniya saboda an gurfanar da ni gaban kotu fiye da karo dubu biyu da dari biyar".