Dakarun gwamnati da na Ouatara sun ja daga a Ivory Coast

an ja daga a Ivory Coast
Image caption Magoya bayan Mr Outtara

Dakarun Ivory Coast sun girke sojojinsu a otel din da Alassane Outtara ya mayar shelkwatarsa, mutuminda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka ta amince da nasararsa a zaben shugaban kasar da aka yi a watan jiya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa an yi harbe harbe.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa, dakarun sojin kasar dake biyayya ga Laurent Gbagbo, wanda ya ki amincewa da shan kaye, sun dora bindigogi masu sarrafa kansu a kan manyan motoci, domin kwace ikon hanyar dake kaiwa ga otel din da Mr Outtara ya ke a Abidjan.

Magoyansa kuma, su ma dauke makamai tare da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na baiwa otel din na sa kariya.