An hallaka jagoran masu satar mutane a Najeriya

Dakarun sojin Najeriya sun ce sun hallaka wani mutum da ake zargin shi ne jagorar kungiyoyi da dama na masu satar mutane da nufin karbar fansa a jihar Abia da ke kudu maso gabashin kasar.

Kakakin sojin ya ce dakarun sun kashe Obioma Nwankwo ne da aka fi sani da Osisikankwu a wata musayar wuta da suka yi a kungurmin dajin Ugwuati a jiya Lahadi.

'Yan sanda a Najeriyar dai sun shafe watanni suna neman Mr. Nwankwo ruwa a jallo bayan da sace-sacen mutane da fashi da makami suka yi kamari a jihar ta Abia.

A cewar wata jarida da ke kasar, Mista. Nwankwo ya yi ikirarin cewa ya shiga satar jama'a ne domin nuna rashin amincewar sa da yadda 'yan sanda ke uzzurawa mutane.

Mutane sun yi murna

Sai dai rahotanni a Najeriyar na cewa mutane sun yi ta murna tun bayanda labarin mutuwarsa ya bazu a gari.

Ana dai samun matsalar sace-sace mutanen a kudu maso gabashin Najeriya, a yayinda masu hannu da shuni da dama suke neman kariyar jami'an tsaro, idan za su tafiya.

Bayan an sace mutanen ana sakinsu ne ba tare da an taba lafiyar su ba, bayan an biya kudin fansa.

An tura wata tawagar jami'an tsaron na hadin gwiwar jihar a watan Satumba, bayan da al'amuran tsaro suka tabarbare a jihar, wanda kuma ya yi sanadiyar sace yaran makaranta.

Daga baya dai an sako yaran, bayan da jami'an tsaron suka tsananta bincike.

Jihar Abia dai tana da yanayin rashin tsaro kamar yankin Niger Delta, inda 'yan bindiga ke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.