Jirgi ya nutse a tekun Antaktika

Hoton jirgin ruwan Korea ta kudun da ya nutse kafin nutsewar tasa
Image caption Jirgin ruwan Korea ta kudu ya nutse

Wani jirgin ruwan Koriya ta kudu mai dauke da mutane arba'in da biyu ya nutse a tekun Antaktika.

Rahotanni sun ce jirgin ya nutse ne a wani waje mai nisan fiye da kilomita dubu biyu kudu da kasar New Zealand.

Hukumomin ceto na kasar sun ce masunta biyar sun rasu, sha bakwai sun bace, sannan kuma ashirin sun tsira da rayukansu.

Cikin masuntan dai akwai yan kasashen Koriya ta kudu, da China, da Indonesia, da kuma Vietnam.