Shugabannin majalisun jihohin Najeriya sun koka

Dimeji Bankole, kakakin majalisar wakilan Najeriya
Image caption Dimeji Bankole, kakakin majalisar wakilan Najeriya

Kungiyar shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya ta nuna rashin amincewarta da wasu gyare gyaren da majalisar wakilai ta kasa ta yi wa dokokin zabe.

A yau ne shugabannin majalisun suka bayyana matsayin nasu, bayan taron da suka gudanar a Abuja.

Daga cikin abubuwan da suke korafi a kai har da kasancewar 'yan majalisar wakilai a kwamitin zartarwa na jam'iyya, da kuma soke sunan 'yan majalisar dokokin jihohi daga cikin wakilan dake halartar manyan tarurukan jam'iyyunsu.

Tun farko dai kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriyar ta dauki irin wannan matsayi, bayan taron da ta gudanar a Abujan.