Kasashe na matsawa Gbagbo kaimin ya sauka

Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara
Image caption Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara

Kasashen duniya na kara matsawa shugaban Cote d'Ivoire, Laurent Gbagbo, kaimin ya sauka ya mika ragamar mulkin kasar ga abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara.

Shugaban hukumar gudanarwar Tarayyar Afirka, Jean Ping, ya gana da mutanen biyu a yau, a kokarin da ya soma na warware rikicin.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon, ya ce dole Laurent Gbagbo ya sauka daga mulki. Idan ba haka ba kwa, duk wata sasantawar da za a yi, ba zata haifar da sahihiyar demokradiyya ba.

A nasa gefen, Praministan Kenya, Raila Odinga, ya ce kamata yayi Tarayyar Afirka ta yi amfani da karfin soji domin tunbuke Mr Gbagbo, yayin da Shugaba Sarkozy na Faransa yayi gargadin cewar, Tarayyar Turai na iya sa masa takunkumi..

Tun lokacin da aka yi zaben shugaban Cote d'Ivoire din a watan Nuwamba ake zaman dar-dar a kasar.

Akalla mutane ashirin sun hallaka jiya Alhamis, a lokacin munanan zanga zangar da aka yi.