Najeriya na shirin sasantawa da Dick Cheney

Dick Cheney
Image caption Dick Cheney

Gwamnatin Najeriya na kokarin cimma yarjejeniya da kamfanin Halliburton, da nufin janye karar da ta shigar a kan tsohon mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney, dangane da wasu tuhumce-tuhumce da take masa da suka shafi cin hanci da rashawa.

Kamfanin ya amince zai biya gwamnatin Najeriyar dala miliyan dari da tamanin a matsayin tara.

A makon da ya gabata ne mahukuntan Najeriyar suka shigar da karar Mr Dick Cheney tare da wasu mutanen takwas, dangane da wasu tuhumce-tuhumce goma sha shidda da suka shafi cin hanci.

Ana zargin kamfanin Haliburton da bayar da toshiyar da ta kai dala miliyon 180, domin ya sami kwangilar dala biliyan 6, ta kafa kamfanin sarrafa iskar gas a Najeriya.