Muharawa kan dokar zaben Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Muhawara kan kudurin dokar zabe

A yau ne ake sa ran majalisar dattawan Najeriya za ta yiwa kudurin dokar zabe ta kasar wadda ta yiwa gyara karatu na uku.

Bayan amincewa da kudirin dokar ne za a mika ta ga wani kwamitin hadin gwiwa da majalisar dattawan da kuma ta wakilai za su kafa don daidaita bambance-bambancen da ke tsakanin dokokin da majalisun biyu suka amince da su.

A makon jiya ne dai majalisar wakilan ta amince da gyaran da ta yiwa dokar zaben, ciki har da bukatar dukkanin 'yan majalisar dokoki ta kasa su zama wakilai a kwamitocin zartarwar jam'iyyunsu, bukatar da ta jawo cece-kuce.

Masu sharhi kan siyasa sun ce, wannan takaddama za ta dada zafafa yanayin siyasar kasar.