Buhari ya yi tsokaci kan rikicin CPC

Janar Muhammadu Buhari
Image caption Buhari ya yi tsokaci kan rikicin jam'iyar CPC

A Najeriya, mai neman tsayawa takarar shugabancin kasa a tutar jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.

Janar Buhari ya ce rikicin ya shafi wasu tsirarun jihohi ne, ba dukkan kasar ba.

Ya kara da cewa, bai kamata wanda ke rike da mukami a jam'iyyar ya tsaya takarar wani mukami(na gwamna, ko shugaban kasa), ba tare da ya ajiye mukamin da ya ke da shi a jam'iyya ba.

Ya ce:''Ba za ta yiwu ba za ka yi takara, kuma ka kasance wanda zai tsara wadanda za su zabi dan takara.Kuma hukumar zabe ta ce duk wanda zai tsaya zabe, sai ya tsaya a takarar fidda-gwani''.

Janar Buhari ya musanta cewa wasu sun shiga jam'iyar ne domin yin amfani da sunansa don lashe zabe, sai dai ya ce mutane na da damar bayyana ra'ayinsu kan hakan.

Jam'iyyar CPC dai ta fada rikici ne tun bayan zabukan fidda-gwanin da ta gudanar a makon jiya.