Yakin basasa na iya dawowa Ivory Coast-inji Ban Ki-Moon

Ban Ki Moon
Image caption Ban Ki Moon

Babban magatakardan Majalissar dinkin duniya, Ban Ki-Moon ya yi gargadin cewar yakin basasa yana iya sake dawowa a kasar Cote D' Ivoire idan dai har aka ci gaba da kiki-kakar siyasar da ake fama da ita yanzu.

Mr Ban ya ce fito na fiton da ake yi tsakanin magoya bayan Shugaban dake kan karagamar mulki da ke da makamai, watau Laurent Gbagbo da kuma mutumin da aka yi amannar shi ne ya lashe zaben da aka yi, Alassane Ouattara, na iya haifar da tashin hankali.

Mr Ban ya sake nanata kiran da yayi na Mr Gbagbo yayi murabus. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kamar 3500 ne suka tsere daga kasar ta Cote D' Ivoire a cikin 'yan makonnin da suka wuce.