Shugaba Jonathan ya gabatar da kasafin kudin 2011

Image caption Shugaba, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gabatar da Naira triliyan 4.236 a matsayin kasafin kudin kasar na shekarar 2011 ga Majalisar Dokokin kasar.

Wannan na nuni da cewa an samu raguwar yawan kudin da za'a kashe bisa kasafin shekara ta 2010.

Shugaba Jonathan wanda zai fuskanci zabe a shekarar 2011, ya ce kasafin kudin na badi ya ragu ne da kashi goma sha takwas cikin darin akan kasafin bara.

Kasafin shekara ta dubu biyu da goma dai ya tsaya ne akan naira triliyan 5.159.

Shugaba Jonathan ya shaidawa 'yan majalisar cewa kasafin na shekara ta dubu biyu da takwas zai taimaka gaya wajen habaka tattalin arzikin kasa da kuma samar da aikin yi.