Kotun manyan laifuka ta duniya ta zargi wasu yansiyasar Kenya su shidda

Luis Moreno Ocampo
Image caption Luis Moreno Ocampo

Babban mai gabatar da kara na kotun kasa da kasa, Luis Moreno Ocampo, ya bayyana sunayen wasu 'yan kasar Kenya shidda da ya ce, yayi imanin sune ke da alhakin tashe tashen hankulan da suka biyo bayan zaben kasar shekaru ukku da suka wuce, inda mutane fiye da dubu daya da dari biyu suka rasa rayukansu.

Mr Ocampo ya nemi alkalan kotun da su tuhimi wadannan mutane shidda da laifukan keta hakkin bil-adama, wadanda suka hada da kisan kai da azabtar da mutane da kuma fyade.

Mutanen sun hada da mataimakin Pirayin Ministan kasar, Uhuru Kenyatta.

A martanin da ya mayar, wanda aka watsa ta gidan talbijin na kasar Kenya, Mr Kenyatta ya ce ba shi da laifi.

Ya ce, " har cikin zuciya ta ba na jin komai, babu wata fargaba a cikin zuciya ta, kuma ba zan samu wata fargaba ba a nan gaba, domin kuwa na san ban aikata wani laifi ba. Rawar da na taka, ita kadai ta isa ta yi min shaida. Bayan zaben 2007 ni da kai na fito ina kira na neman zaman lafiya".