Shugaba Jonathan ya bayyana kasafin kudi

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban majalissar dokokin kasar.

Shugaba Jonathan ya gabatar da kasafin kudi na fiye da Naira Tiriliyan 4.

Ya ce wannan kasafin kudi na nuni da babban zabtare kudaden da aka amince a kashe cikin shekara ta dubu 2 da 10.

Shugaban ya ce, kasafin kudin na 2011, kasafin kudi ne na daddale harkokin kudi da kara yalwar tattalin arziki da kumasamar da aikin yi.

Ya ce, an tsara kasafin kudin ne tare da yin hasashen farashin mai zai kasance a kan Dola 65 a kan kowace ganga, tare kuma da hako ganga miliyan 2 da dubu dari 3 a kowace rana, sannan kuma da musayar Dola daya ta Amurka a kan kudin kasar na Naira 150.

Masu aiko da labarai sun ce babbar matsalar tattalin arzikin Nigeria, har kwanan gobe ita ce gibin kasafin kudin da ake samu, abun da ke rage kimar kasar wajen samun basussuka daga kasashen waje.

Gabanin wannan kasafin kudi dai, Gwamnan Babban bankin Nigeria, Malam Sanusi Lamido Sanusi, ya koka akan yawan kudaden da ake kashewa a kan yan majalisun dokoki na kasar.