Rikici a jam'iyyar ACN

Tutar jam'iyyar ACN
Image caption Rikici a jam'iyyar ACN

A Najeriya, baraka ta kunno kai a cikin jam'iyyar adawa ta ACN a jihar Gombe inda wasu 'yan jam'iyyar ke barazanar zuwa kotu bisa zargin rashin yi masu adalci.

Wannan lamari ya biyo bayan zabukan shugabannin jam'iyyar da aka yi ne, abin da ya sa bangarori biyu na jam'iyyar su ka gudanar da zabuka daban-daban, kuma a rana guda.

Kowanne bangare na ikirarin cewa nasa zaben ne halattacce.

Hakan na faruwa ne a lokacin da kasar ke tunkarar babban zaben da za a gudanar a badi.