An yi arangama a Cote D'voire

Fito na fito tsakanin yan sanda da masu zanga zanga
Image caption Fito na fito tsakanin yan sanda da masu zanga zanga

Rahotanni daga Ivory Coast sunce mutane akalla 9 ne aka kashe a lokacin da dakarun tsaro suka yi kokariin tarwatsa wata zanga zanga da magoya bayan Alassane Ouattara suka yi a Abidjan.

An ji amon bindigogi a ko'ina cikin birnin. An fara tashin hankalin ne a lokacin da magoya bayan Alassane Ouattara suka yi kokarin kwace iko da gidan Talbijin na kasar.

Haka nan kuma an bada rahoton yin artabu a tsakiyar kasar ta Ivory Coast tsakanin tsoffin mayakan 'yan tawaye da dakarun dake biyayya ga shugaban kasa mai ci, Laurent Gbagbo, wanda ya hakkake shi ne ya lashe zaben na watan jiya.

Za'a iya bayyana rikicin siyasar na Ivory Coast a matsayin wata manuniya ta baya bayan nan game da irin gwagwarmayar dora kasar kan tafarkin dimokradiyya a daya daga cikin kasashe masu muhimmanci a Yammacin Afirka.

Shugaban kasar Mai ci, Laurent Gbabo, ya ki sauka daga kan mulki, duk da cewa kasashen duniya da dama sun bayyana mai adawa da shi watau Alassan Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.