'Yan sanda sun tsare tituna a Katsina kan takarar Masari

A Nijeria, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta rufe yawancin hanyoyin shiga da fita daga jihar, a yayinda tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Alhaji Aminu Bello Masari ke kaddamar da neman takararsa ta gwamna a karkashin jamiyyar adawa ta CPC.

'Yan sandan dai sun ce sun dauki wannan matakin ne don kaucewa tashin hankali a jihar.