Nigeria ta baiwa Niger agaji kan zabe

Salou Djibo
Image caption Shugaban gwamnatin mulkin sojin Niger

Gwamnatin Nigeria ta baiwa jamhuriyar Niger dollar miliyan 5 a matsayin agaji domin tallafawa kasar ta gudanar da zabubbukan mayar da kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.

Wannan tallafi ya zo ne a lokacin wata ziyara da manya manyan jami'an tsaron Nigeria suka kai zuwa Jamhuriyar Niger.

Tawagar ta Nigeria ta kunshi mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, watau Janar O. A. Azazi da kuma babban sufeto janar na 'yan sandan Nigeria, Alhaji Hafiz Ringim.

Alhaji Hafiz Ringim ya bayyana cewar Nigeria ta bayar da wannan taimako ne a matsayin abokiyar kawancen jamhuriyar Niger tare da fatan zaa kammala zabe lami lafiya, domin duk abun da ya shafi Niger ya shafi Nigeria.