Rashin adalci a Afghanistan

Taswirar Afghanistan
Image caption Rahoto kan rashin adalci a Afghanistan

Wani sabon rahoto da aka fitar a London ranar alhamis ya ce rashin tabbatar da adalci daga wajen shugabanin Afghanistan, shi ke kara hare-haren kunar bakin-waken da kasar ke fama da shi.

Rahoton, wanda wata cibiyar dake gudanar da bincike, wadda ke Birnin London ta fitar, ya ce wanzuwar adalci shi ne ya kamata gwamnatin Afghanistan ta baiwa muhimmanci idan tana son zaman lafiya.

Shekaru da dama bayan rushewar gwamnatin Taliban, da alama a yanzu,babu wani tsari na tabbtar da adalci a kasar.

Kuma hakan ya yi sanadiyar wanzuwar cin hanci, da nuna bambance-bambance.

Rahoton ya kara da cewa ko da kuwa yafewar da 'yan siyasa suka yiwa juna bata tsinana komai ba, illa ma kara nuna yadda jama'ar kasar ke tsanar juna.

Rahoton ya ce rashin tabbatr da adalcin ya sa jama'a na cewa, hankalin su ya fi kwanciya karkashin gwamnatin Taliban.

An fitar da wannan rahoto ne, a yayin da gwamnatin shugaba Obama na Amurka ke dab da fitar da wani rahoton kan irin ci gaban da ake samu a yakin na Afhanistan.