Nazari: Amurka na samun nasara a Afghanistan

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama na fatan kara samun nasara kan Al-qa'ida

Wani babban nazarin manufar Amurka a Afghanistan ya ce karin yawan dakarun kawance da aka yi kwanan nan ya yi nasarar murkushe tasirin Taliban a galibin kasar.

To amma kuma ya yi gargadin cewar waccan nasara har yanzu ba ta da karfi, kuma za a iya rasa ta.

Nazarin ya ce a halin yanzu manyan Shugabannin Al-Qa'ida a Pakistan sun yi rauni, kuma suna cikin matsi matuka fiye da duk wani lokaci tun faduwar Taliban shekaru goma da suka wuce.

Amurka za ta soma rage dakaru a badi -- kuma ana sa ran kawo karshen yakin da take yi a cikin shekara ta 2014.