Najeriya ta janye tuhuma a kan Dick Cheney

Image caption Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney

Hukumomi a Najeriya sun janye tuhumar da su ke yiwa tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, da wasu jam'ian kamfanin Halliburton, ta yunkurin bada cin hanci ga wasu jam'ian gwamnatin kasar, domin samun kwangilar gina wani kamfanin iskar gasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Mr. Cheney ke shugabantar Halliburton. Bangarorin biyu sun sasanta ne a wajen kotu, kan wasu kudade da yawansu ya kai dala miliyan dari biyu da hamsin.

Kakakin hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta EFCC, Mr. Femi Baba femi ya tabbatar mini da cewa gwamnatin Najeriyar ta janye karar da ta shigar gaban wata kotu a Abuja, kan zargin da ake wa tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney.

Mr. Femi ya kara da cewa janye karar ya shafi Mr. Cheney ne da wasu su takwas da suka hada da wasu jami'an katafaren kamfanin na Hallibatun da kuma wasu kamfanoni da aka shigar gaban kuliya tare, game da ba da cin hanci ga wasu jami'an gwamnatin Najeriya don samun kwangila.

Ya kara da cewa janye karar bai shafi sauran shari'oin da ake ba na zargin wasu 'yan Najeriyar da hannu a wannan badakala.

Janye kara da tuhumar da akewa Mr. Cheney dai ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a wajen kotu na biyan gwamnatin Najeriyar dala miliyan 250.

A ranar farkon wannan watan ne hukumar ta EFCC, ta tuhumi tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Dick Cheney a kotu da laifin yunkurin bayar da cin hancin dala miliyan dari da tamanin ga wasu jami'an Najeriya domin samun kwangilar gina cibiyar sarrafa iskar gas ta dala biliyan tamanin.

Hukumar dai ta tuhumi Dick Cheney ne kasancewar shi ne shugaban kamfanin Halliburton a lokacin da ake zargin an bada cin hancin.