Sufeto Janar ya soki 'yansandan Najeriya

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya ya ce 'yan sanda a yankin arewa maso gabashin kasar sun kasa gudanar da ayyukansu don sun kasa samar da tsaro ga mazauna yankin daga hare-haren mutanen da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Sufeto Janar na 'yan sandan na Najeriya, Hafiz Ringim, ya bayyana gazawar da 'yan sandan suka yi wajen kare jama'a da cewa babban abin kunya ne.

Rahotanni sun kuma ambato Sufeto Janar din yana mamakin yadda 'yan kungiyar ta Boko Haram suke sanin irin matakan tsaron da 'yansanda ke dauka, da kuma yadda jami'an 'yansandan suka kasa gano maboyar 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Wannan ne dai karo na farko da Sufeto Janar din ya fito karara ya soki jami'ansa da rashin tabuka wani abin-a-zo-a-gani wajen magance matsalar ta Boko Haram.

A 'yan watannin da suka gabata dai wadansu wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun hallaka sama da mutane talatin, cikinsu har da jami'an tsaro, da shugabannin al'umma, da ma na addini.