Ana kara matsin lamba a kan Laurent Gbagbo

Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara
Image caption Laurent Gbagbo da Alassane Ouattara

Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast na fuskantar karin matsin lambar kasashen duniya kan ya sauka daga kujerar iko yayinda ake kara nuna damuwa a kan yiwuwar sake jefa kasar cikin yakin basasa.

Laurent Gbagbo da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, sun yi ikirarin lashe zaben da aka gudanar a kasar a watan Nuwamba.

Tuni dai wannan takaddama ta jawo tashe-tashen hankula a titunan Abidjan, babban birnin kasar, wadanda mutane suka kaurace musu.

Mutane da dama dai na tsoron fita ne bayan taho-mu-gamar da ta biyo bayan yunkurin da magoya bayan Alassane Ouattara suka yi na karbe iko da gidan talabijin na gwamnati.

Mista Ouattara dai na samun goyon bayan kasashen duniya a ikirarinsa na cewa shi ne ya lashe zaben.

To amma Mista Gbagbo, wanda ya kwashe shekaru goma yana mulki a kasar mai arzikin cocoa, ya kankame madafun iko; kuma har yanzu sojojin kasar na tare da shi.

An shirya zaben ne dai da nufin hade kan kasar bayan yakin basasar 2002 da kuma 2003 wanda ya raba tsakanin arewaci—inda Musulmi suka fi rinjaye—da kuma kudanci—inda Kiristoci suka fi rinjaye.

Faransa, wadda ta yiwa kasar mulkin mallaka, ta yi kira ga Mista Gbagbo ya sauka kafin karshen mako ko kuma ya fuskanci takunkumi.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, shi ma ya yi kira ga Mista Gbagbo ya sauka, yayin da Firayim Ministan Kenya, Raila Odinga, ya ce ya kamata kasashen duniya su shirya yin amfani da karfin soji don kawar da shi.